1 Janairu 2026 - 14:05
Source: ABNA24
Sheikh Yakub Ya Rufe Mu'utamar ’Yan Midiya A Katsina + Hotuna

Sheikh Yakub Yahya Katsina, ya rufe mu'utamar na yini ɗaya, wanda dandalin yaɗa labarai na 'yan uwa musulmi almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) na yankin Katsina suka shirya, a ranar Lahadi 08, Rajab, 1447, daidai da 28, Disamba, 2025, a muhallin Markaz Katsina.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A cikin jawabin da su Malam suka gabatar, sun ja hankalin ’yan mediyar akan muhimmancin yaɗa labarai a wannan zamanin.

“Duniyar nan ana juya ta ne da kafafen watsa labarai, kuma da haka ake tafiyar da ita, kamar yadda Imam Khumaini (Q.S) ya faɗa. "Ku sa ni duniyar yau ana juya ta ne, ta hanyar kafafen yaɗa labarai, alhali mu gashi kafafen yaɗa labaran mu, su na da rauni "A lokacin fa akwai gwamanti a hannu, akwai gidajen rediyo, akwai gidajen talabijin, amma yana ganin cewa suna da rauni, akwai kafafen yaɗa labarai ta fuska daban daban, amma duk da haka yana ganin shi da rauni.”

Sheikh Yakub Yahya Katsina, ya ƙara yi ma mahalarta taron bayanin yadda aka yi amfani da kafafen watsa labarai wajen haddasa rikici a cikin kasar nan.

“Yanzu ga shi ta hanyar kafafen watsa labarai kunga irin matsalolin da suka antayo mana a cikin kasar nan. Sun yi amfani da kafafen watsa labarai sun ƙirƙiri wasu mutane wai sunan su ’Yan Ta'adda (Kuma duk mun yarda ’Yan Ta'adda ne). Sun ƙirƙiri wasu mutane sun ce sunan su Lakurawa (Kuma duk mun yarda Lakurawa ne) alhali su suka samar da kayan su, kayan su ne, su suka samar su ka sako ma na, sun kuma ƙirƙira mutane sun kai su daji sun ce ’Yankidinafas (Kuma duk mun yarda ’Yankidinafas ne), sun ƙirƙira ma na matsala, sun ce akwai matsala tsakanin Fulani da Hausawa”.

Su Malam sun cigaba da bayani akan kiyaye abin da za a rubuta domin gudun tsayawa kare kai gaban Allah (SWT).

“Abu na farko shi ne yi don Allah, wannan kuma kalma ce da su Malam Hafizahullah suka sha maimaitawa cewa ayi don Allah, saboda duk abin da zamu yi ya zama don Allah ne muka yi shi, muna wakiltar addini ne, muna isar da sakon addini, saboda haka duk abin da zamu rubuta ya zama gaskiya ce muka rubuta, kuma ya zama mutum zai iya kare abin da ya rubuta a gaban Allah. Da za a tambaye shi (Saboda da rubutu da magana abu guda ne) zai iya kare kanshi, ya zama duk abin da ka rubuta zaka iya kare kanka a gaban Allah domin za a tambaye ka”.

Sheikh Yakub Yahya Katsina ya jaddada muhimmancin haɗuwa ayi aiki tare, sannan kuma a tafi tare da kowa, ba tare da yin wariya ba, sannan kuma abi nizami, inda ya bayyana muhimmancin murya ɗaya a cikin al'umma. Sannan daga ƙarshe ya yi nasiha ga 'yan uwa akan kauce ma dukkan wani abu da ya ke kawo cece-kuce a kafafen soshiyal mediya.

“A ba da dama mutane su faɗi ra'ayoyin su, kada a hana kowa faɗin ra'ayinsa, Amirul-Mumunina (AS) yace: "A ɗauko ra'ayin wancan, a ɗauko ra'ayin wancan a haɗa su waje ɗaya, sai aga gaskiya ta fito. Wannan ya faɗa, wannan ma ya faɗa sai a gane ina gaskiya ta ke, amma idan aka hana wani ya faɗi gaskiya, ko aka danne wani ya faɗa to ina gaskiya zata fito?”.

“Sannan kuma a guji sa-in-sa, akwai sa-in-sa ko? Ana yin sa-in-sa, ana yin cece-kuce. Lallai yakamata mai addini ya shagaltu da addini. Dan Allah a bar ma cece-kuce soshiyal mediya ta yi ta abin ta, ba aikin mu ba ne. Allah ta'ala yace: "Ma su san alfasha (Mummunan aiki) ya yaɗu a cikin Muminai, to Allah ya yi masu mummunan alkawari" to ka da mu zama cikin masu san mu yaɗa mummuna, ta yiyu ma wani ya baka aiki, kai baka sani ba”.

“Abin da basu so shi ne aiki na Iklasi, (Ka tsaya kasan mi ka ke, kuma ka cigaba da abin da ka ke, ba tare da waiwaye ba) to shi ne ke basu so, to idan kayi haka to kafi basu haushi, shi ne ke basu so, ya fi ban haushi, saboda su ba haka suke so ba, so suke a daina komi a zauna ayi ta cece-kuce. Saboda haka a guji cece-kuce”.

"Muna da aiki gaban mu, kunga America ta shigo ko, to duk ku aje komi muyi aikin dake gabanmu. Kunga al'ummar mu bata san komi ba, al'ummar mu abin tausayi ce, bata san wanene masoyin ta da macucin ta ba. Tuwo kawai ta sanya a gaba.

Your Comment

You are replying to: .
captcha